Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da ke Jihar Borno,inda ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida.
Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba.
An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta Jiha nan take, yayin da ƙungiyoyin sintiri ƙarƙashin jagorancin DPO na Mafa suka taimaka wajen daƙile cunkoson jama’a da kuma hana satar kayayyaki.
- An Hallaka Manoma 40 a Jihar Borno
- Gwamnatin Borno ta fara yunƙurin gyara tsarin birnin jihar domin kiyaye ambaliyar ruwa
- Sojoji sun kashe ‘yan ta’addan ISWAP 15 a Borno
Rahotanni sun nuna cewar an kashe gobarar ba tare da an samu rahoton raunuka ko asarar rayuka ba.
Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da suka lalace ba, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin gobarar.
