Wata gobara ta kone shaguna da motoci a babbar kasuwar kayan motoci da ke Sakkwato, wadda aka fi sani da Garejin Buzaye, da safiyar Litinin.
Rahotanni daga wurin sun bayyana cewa gobarar ta yi sanadiyar lalacewar shaguna da motoci da sauran kadarori, duk da ƙoƙarin da Hukumar Kasar ta kashe gobara da mazauna yankin suka yi.
Ana zargin gobarar ta samo asali ne daga matsalar lantarki, inda wutar ta shafe sa’o’i kafin a samu damar kashe gobarar.
Wani mai gyaran mota a kasuwar ya bayyana cewa akalla shaguna 40 ne suka salwanta, ciki har da wuraren gyaran motoci irin su Marsandi da shagunan sayar da kayan ajiya.
Wasu daga cikin motocin da gobarar ta shafa daga Jihar Sakkwato ne, yayin da wasu kuma daga ƙasar Jamhuriyar Nijar suke.
Shugaban ƙungiyar Kanikawa ta ƙasa reshen Garejin Buzaye, Injiniya Abdulkadir Muhammad, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki, sannan ya roƙi gwamnatin Jihar Sakkwato da ta kai tallafi ga waɗanda abin ya shafa.
