Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sunusi II, ya fara daukar Darasi a jami’ar Northwest University Kano a yau Talata.
Hakan ya biyo bayan samu gurbin karatu da Sarkin Kanon, ya yi a Jami’ar Northwest University, Kano, kamar yadda jami’ar ta sanar.
A wata takarda da shugaban Sashen Jarrabawa Karɓar Dalibai da adana bayanai Jafaru Sule Muhammad, ya sanya wa hannu a madadin Magatakarda an bayyana cewa Sarkin ya samu gurbin karatu a fannin Shari’a a matakin Level 200, daga zangon karatu na 2025/2026.
Takardar wacce aka aika zuwa Gidan Rumfa Kano ta na fatan Sarkin da ya kasance mai bin duk wasu ƙa’idoji da dokokin makarantar kamar yadda aka tanada a cikin kundin gudanarwar ɗalibai.
