
Najeriya ta gamu da cikas a ƙoƙarinta na neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya na 2026, bayan da ta tashi 1-1 da Zimbabwe a ranar Talata.
Victor Osimhen ne ya fara ci wa Najeriya kwallo a minti na 74 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo a jihar Akwa Ibom.
Zimbabwe ta farke ana daf da tashi a minti na 90 ta hannun ɗan wasanta na gaba, Taranda Chirewa.
Wannan sakamako na nufin cewa Najeriya na mataki na huɗu a rukunin C, inda Ghana ke gabanta a matsayi na ɗaya da kusan ratar maki shida bayan buga wasanni shida.
Wasan da Najeriya za ta yi da Bafana Bafana ta Afrika ta Kudu a watan Satumba, zai kasance mai matukar muhimmanci – Ganin cewa ƙasar da ke saman kowane rukuni ne kaɗai ke samun damar zuwa gasar kofin duniya.