Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce da yana da damar ba tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, shawara kafin tsare shi, da ya buƙace shi ya ci gaba da zama a jam’iyyar APC tare da rage yawan magana.
Yahaya Bello ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce yana mutunta basira da jajircewar El-Rufai, duk da cewa sun shafe sama da shekaru huɗu ba tare da tattaunawa ba.
Ya ce da suna da kyakkyawar hulɗar da suke da ita a baya, da ya shawarci El-Rufai ya ci gaba da kasancewa a APC, tare da barin Shugaba Bola Tinubu ya yanke shawarar yadda zai tafiyar da matsalolin siyasar da ake fuskanta.
An dai tsare El-Rufai ne a watan Fabrairun 2026 bayan gayyatarsa da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta yi, kan zarge-zargen almundahana da suka shafi lokacin da yake gwamnan Kaduna.
Sai dai Yahaya Bello ya bayyana fatan El-Rufai zai shawo kan matsalolinsa, yana mai cewa yana masa fatan alheri.
