Majalisar Wakilai za ta ƙada kuri’a a ranakun 10 da 11 ga watan Disamba kan muhimman kudurorin gyaran kundin tsarin mulkin 1999, ciki har da kirkirar sabbin jihohi da kafa ’yan sandan jihohi.
Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Okezie Kalu, ya sanar da jadawalin a zaman majalisar, inda ya ce tattaunawa kan kudirin sauya kundin tsarin mulki za ta gudana yau da gobe kafin kada kuri’ar mako mai zuwa.
Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar kan nazarin kundin tsarin mulki, ya bukaci ’yan majalisa su halarci zaman.
A farko dai an gabatar da jimillar kudirori 87 da ke neman sauya sassa daban-daban na kundin tsarin mulki.
Sai dai bayan jin ra’ayin jama’a a matakin jihohi, taron jin ra’ayin jama’a na kasa a Abuja, tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma daidaitawa da kwamitin majalisar dattawa kan kundin tsarin mulki, adadin kudirin da za a kada kuri’a ya ragu zuwa kusan 45.
A ranar Litinin, 24 ga watan Nuwamba, kwamitocin majalisar wakilai da na majalisar dattawa kan gyaran kundin sun gudanar da taron hadin gwiwa da kakakin majalisun jihohi a Abuja yayin da tsarin sauya kundin ya shiga matakin karshe.
Kalu da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, sun shaida wa kakakin majalisun jihohi cewa makomar kudirin sauye-sauyen yanzu ta dogara ne da majalisun jihohi bayan majalisar tarayya ta kammala aikinta.
