Hukumar Leken Asiri ta Soja DIA ta ƙara tsananta bincike kan zargin shirin kifar da gwamnatin Tinubu.
Jami’an tsaro sun fara tambayar wani Darakta-Janar na wata hukumar gwamnatin tarayya kan wata mu’amalar kuɗi da ake zargi tana da alaka da lamarin.
An kama wannan Darakta-Janar ɗan asalin Yankin Kudu maso Kudu, bayan ya tura wasu makudan kuɗaɗe zuwa ga tsohon Ministan Man Fetur kuma tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva.
Da yanzu ake bincike a matsayin ɗaya daga cikin wadanda ake zargin suna da hannu a shirin kifar da gwamnati, A cewar Jaridar Newspoint, dogaro daga majiyoyinta a hukumomin leken asiri.
Masu bincike suna zargin cewa kuɗin an aika su ne domin aiwatar da juyin mulkin.
Rahotanni sun ce, binciken ya ƙara tsananta ne a ƙarshen mako, lokacin da jami’an soja suka kai samame a asirce a gidan Sylva a Abuja.
A lokacin samamen Sylva ba ya ƙasar, sai dai an kama ƙaninsa mai suna Paga, wanda shi ne mai taimaka masa kan harkokin cikin gida da kuma direbansa.
Bayan samun labarin kamen ne, Sylva ya janye shirin dawowarsa, In ji jaridar.
