
Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta fara gudanar da bincike kan hatsarin motar da ya kashe mutum 22 daga tawagar ’yan wasan Jihar Kano yayin da suke dawowa daga Gasar Wasanni ta Ƙasa da aka kammala a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Hukumar ta ce, wajen da hatsarin ya faru ya yi ƙaurin suna da yawan faruwar haɗuran mota.
Shugaban FRSC na ƙasa, Shehu Mohammed, ya bayyana hakan lokacin da ya kai wa Gwamnatin Jihar Kano ziyarar jaje a ranar Litinin.
Ya kuma ce, hukumar ta fara bincike kan dalilan da afkuar hatsarin, za kuma ta gabatar da sakamakon binciken ga hedikwatarta da kuma Gwamnatin Jihar Kano domin ɗaukar matakan da suka dace don hana faruwar irin wannan iftila’i a gaba.
Hukumar ta kuma sake jaddada ƙudirinta na wayar da kan al’umma kan amfani da hanya yadda ya dace da kiyaye lafiyar masu amfani da hanya.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Gwarzo, ya wakilta, ya gode wa FRSC bisa ziyarar.