
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi reshen jihar kano NDLEA, tace an samu nasarar raguwar ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar kano a ‘yan kwanakin nan.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar Sadiq Muhammad Maigatari ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da wakiliyar mu Halima Ayyuba Adamu, inda yace nasarar ta biyo bayan kafa kwamitin wanzar da zaman lafiya da inganta tarbiyar matasa dfa gwamnatin Kano tayi
Maigatari ya ce kwamitin ya kunshi duka jami’an tsaron jihar kuma ana samun nasara sosai musamman fadan daba da ake fama dashi shima ya ragu.
Ya ce a baya jihar Kano na a matakin farko a harkar shaye shaye a kasar nan, amma a yanzu batun ya sauya.
A bayan nan ne dai hukumar NDLEA ta samu nasarar kamo wani dilan kwaya a cikin sumamen da kwamitin ta kai na tsahon kwana uku, inda suka kamashi a kasuwar Yakasai suna saida miyagun kwayoyi.