
Kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) ta bayyana cewa matsalar yunwa na ƙara kamari a yankin Arewa maso Gabas, musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe, inda fiye da mutane miliyan 3.7 ke fama da matsanancin rashin abinci.
A wani rahoto da ta fitar, ICRC ta ce rikicin Boko Haram da ya ɗauki sama da shekaru 16 ya lalata kasuwanci da hanyoyin samun aiki, lamarin da ya tilastawa jama’a dogaro da ƙananan gonaki don ci gaba da rayuwa.
A garin Dikwa na jihar Borno, manoma na tashi da sassafe suna ratsa hanyoyi masu nisa domin yin noma na ‘yan awanni kafin su koma gida, a cewar rahoton.
Shugabar ofishin ICRC a Maiduguri, Diana Japaridze, ta bayyana cewa daga watan Yuli zuwa Satumba ana fuskantar babban haɗarin ƙarancin abinci, inda jama’a ke buƙatar siyan abinci, amma rashin kuɗi na hana su iya biyan bukatunsu.
Don rage tasirin matsalar, ICRC ta fara wani shiri na taimaka wa manoma ta hanyar raba iri da kayan aikin noma ga fiye da iyalai 21,000 a bana, domin tallafa musu a lokutan kaka da rani.