Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa jam’iyyun siyasa guda goma 10 ne za su shiga zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano, wanda aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga watan Fabrairu.
Kwamishinan Zaɓe na Jihar Kano, Ambasada Abdu Zango, ne ya bayyana hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a birnin Kano.
Ambasada Zango ya ce hukumar ta karɓi sunayen ’yan takara daga jam’iyyun guda goma da za su fafata a zaɓen kujerun Majalisar Dokokin Jiha da ke wakiltar ƙananan hukumomin Birni da Ungogo.
A cewarsa, jam’iyyun da za su shiga zaɓen sun haɗa da APC, ADP, AAC, PRP, LP, APGA, NNPP, da dai sauransu.
Ya ƙara da cewa hukumar ta INEC ta sanya ido sosai kan yadda jam’iyyun suka gudanar da zaɓukan fidda gwani, inda ya bayyana cewa ba a samu rahoton wata matsala ba.
Kwamishinan Zaɓen ya kuma bayyana cewa ƙananan hukumomin Birni da Ungogo suna da fiye da masu rajistar zaɓe 535,000, tare da rumfunan zaɓe sama da 1,000.
