Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar kare hakkin masu saye ta kasa (FCCPC) ta kulle wasu guraren ajiye kaya a rukunin kamfanoni na Sharada da wasu sassan masana’antu a nan Kano.
FCCPC ta kulle guraren ne yayin samamen da ta kai ranar Laraba biyo bayan bayanan sirri kan zargin guraren da algus da adana kayayyakin bogi.
Da take jawabi ga manema labarai daraktan sashen bincike ta hukumar Boladale Adeyinka, lefukan da ake zarginsu da aikatawa sun saba da sashe na 123 da 125 na dokokin hukumar.
Boladale Adeyinka ta bukaci al’umma da su kai korafin duk wani shago, kamfani, ko masana’anta da ke aikata zamba ko tauye hakkin masu saye ga hukumar ta FCCPC.
Ta ce akwai tara ko dauri ga masu yin almundahana a harkokin kasuwanci.
Ta ce duk wanda aka samu da laifi dauri yana kamawa daga shekara 5 zuwa 10 ko tara daga miliyan 5 zuwa 100 ko a hadawa mutum gaba daya.
