Tayar jirgin kamfanin ta fashe ta kuma kama da wuta a yayin da yake kokarin sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:45pm na daren Talata, a cewar wani fasinja da ke cikin jirgin da ya sauka da kyar.
Sai dai fasinjan Aliyu Inuwa ya kara da cewa tuni aka gaggauta kwashe fasinjojin daga jirgin ba tare da rahoton samun rauni ba a cikinsu.
Jirgin mai lamba jigila VM1605 da kuma lambara rajistar aiki 5N-MBD ya taso ne daga Lagas zuwa Kano na dauke da fasinjoji 53.
Manajan kamfanin jirgin na Kano, Malam Bello Ramadan ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ba a samu asarar rai ba.