
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta shigo da kayayyakin gwangwan daga yankin Arewa maso Gabas zuwa cikin jihar, a wani mataki na dakile barazanar tsaro da ke kara ta’azzara a baya-bayan nan.
Kwamishinan Tsaro na jihar Kano, AVM Ibrahim Umaru (mai ritaya), ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Kwamishinan ya ce, matakin ya zama dole ne biyo bayan wasu fashe-fashe da suka faru a jihar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar tare da jikkatar wasu da dama.
“Binciken da hukumomi suka gudanar ya nuna cewa bama-baman da suka tashi a cikin Kano, an shigo da su ne cikin kayayyakin gwangwan daga yankin Arewa maso Gabas ne, yanki da ke fama da rikicin Boko Haram tun shekaru da dama.
Kwamishinan ya jaddada cewa wannan mataki na gwamnati na da nufin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da dakile duk wata barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.
Ya kuma gargadi ‘yan kasuwa da masu safarar irin wadannan kayayyaki da su kiyaye dokar, yana mai cewa duk wanda aka samu da karya ta zai fuskanci hukunci mai tsanani.