Jamiar Cite dake kasar Faransa ta karrama shugaban gamayyar Jami
oi masu zaman kansu na Afrika Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo da lambar girmama dangane da irin sadaukarwar da yake da taimakon harkar Ilmi a kasashen Afrika.
A Jumaar nan ne dai aka gudanar da bukin karramawar da Jami
ar ta Cite dake kasar ta faransa ta baiwa farfesa Gwarzo karramawar wanda kuma har wayau ke zaman shugaban gamayyar Jamiar Maryam Abacha University, wanda bukin ya samu halartar wakilin KWAMITIN Ilmi na Majalisar Dinkin Duniya. Shugaban jami
ar ta Cite Senator Jean Mac Sauve ya bayyana cewar jamiar ta zabi data abiwa farfesa Adamu gwarzo wannan Lambar girmamawar ne, musamman la
akari da yanda yake taimakon Ilmi, ba dare ba rana, tare da bada dukka gudunmowar data kamata wajan cigaban ilmi a yankin Afrika.
Taran bada lambar yabon ga mashahuran mutane a Duniya yazo dai dai da lokacin da Jamiar ke cika shekaru 100 da kafuwarta wanda ta shirya taruka daban daban da suka shafi ilmi da ganawa da manyan jami
ai da suka shfai ilmi a DUniya da nufin sake bunkasa harkar dan goben masu tasowa.
A yayin jawabinsa SHugaban Jamiar ta Cite Senator Jean Mac Sauve ya bayyana cewar sunyi matukar farin ciki da yadda farfesan ke bunkasa Ilmi a Afrika, wanda daman tsohon dalibin Jami
ar ne, yana mai cewar farfesa Adamu gwarzo ya ciri tuta tsakanin wadanda suka kai suka kawo da nufin cicciba ilmi zuwa mataki na gaba.
