Ana hasashen saukowar farashin man fetur a Najeriya sakamakon sanar da soma fitar da man fetur da kuma dagoginsa daga matatar mai ta Fatakwal
Kamfanin NNPCL a ranar Talata ya sanar da soma aikin matatar gadan-gadan a inda zai rikar samar da man fetur da dizal da kuma kananzir da sauransu.
A yanzu kimanin manyan motoci 100 ne ke lodin man kuma matatar na da burin samar da manyan motoci 200 a kullum.
’Yan kasuwa sun yi marhabin da fara dakon tataccen mai daga matatar ta Fatakwal, inda suke sa ran hakan zai kawo gasa da inganci da kuma faɗuwar farashin man a kasa baki daya.
A halin yanzu kusan motoci 100 ne ke lodin man daga matatar ta Fatakwal zuwa sassan kasar nan bayan watanni 11 da soma gyaranta.
Kungiyar Manyan Masu Kasuwar Makamashi ta Najeriya (MEMAN) ta yi imanin cewa yalwar man zai kawo raguwar farashinsa.
Ita ma Kungiyar Dillalan Man Fetur Mai Zaman Kanta Ta Najeriya (IPMAN) ta yi marhabin da wannan ci-gaba.
Shugaban Kamfanin na NNPC Mele Kyari ya ce, wannan wata babbar nasara ce ga kasar nan wanda hakan ya bude wani sabon babi na wadatar makamashi da kuma bunqasar tattalin arziki.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya kamfanin NNPCL murna da wannan namijin kokari sannan ya bukaci a gaggauta farfaɗo da matatar mai ta Kaduna da kuma ta Warri.
Domin bunƙasa samar da mai a cikin gida da kuma mayar da Najeriya babbar cibiyar samar da makamashi.