
Farashin Dalar Amurka a kasuwar canjin kudi ya sauka zuwa Naira 1,500 a kasuwar hada-hadar kudaden waje a kasar nan.
Masu sana’ar canjin kuɗi a Wapa sun alaƙanta saukar farashin Dalar Amurka da matakan da Babban Bankin Kasa CBN ya dauka wajen karya Dalar.
Ciki har da sahalewar da gwamnati ta yiwa dillalan man fetur amfani da naira maimakon Dala.
Shugaban kasuwar Alh. Sani Salisu Dada ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da wakilinmu Primier Radio a ranar Juma’a.
“Tsawon makwanni farashin Dala ke ci gaba da sauka, inda ake musayar da ita a ranar Alhamis a Naira 1,500.
“Duk da saukar da farashin Dalar ke yi bai shafi kasuwancinsu ba, domin su na gudanar da shi kamar yadda suka saba”. In ji shi.
Masana tattalin arziki na ganin cewa matukar gwamnati ta ci gaba da bijiro da hanyoyin da za su karya Dala, babu shakka Naira za ta samu tagomashi.
Wanda hakan zai sa al’ummar kasar nan su samu saukin rayuwa tare da bunkasar tattalin arziki.