
Kwamitin Raba Tattalin Arziki na Ƙasa (FAAC) ya raba jimillar Naira tiriliyan 1 da biliyan 659 ga Gwamnatin Tarayya da Gwamnatocin Jihohi da kuma na Kananan Hukumomi a watan Mayu 2025.
Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ofishin Babban Akanta na Ƙasa ya fitara bayan taron watan Yuni da aka gudanar a Abuja.
Sanarwar, wadda Daraktan Hulɗa da Jama’a na ofishin, Bawa Mokwa ya sanya wa hannu ta bayyana cewa an tara jimillar Naira tiriliyan 2.942 a watan Mayu, amma an ware Naira biliyan 111.908 don biyan kuɗin tara haraji da Naira tiriliyan 1.171 domin tallafi da sauran ayyuka kafin rabon.
FAAC ya ce, karin kuɗin shiga ya samo asali ne daga harajin kamfanoni (CIT), harajin kaya (VAT), da na kaya da ake shigo da su daga waje. Duk da haka, an samu raguwa a kuɗaɗen da ake samu daga harajin man fetur da na lantarki.
Rabon kason kudin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan bunkasa hanyoyin samar da kuɗin shiga da kuma rage dogaro ga man fetur a matsayin tushen kudin shiga ga ƙasar.