Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano a bainar jama’a, karon farko tun bayan dawo da shi sarauta.
Ganduje ya yi wannan furuci ne a Fadar Gwamnatin Kano yau Talata yayin rantsar da sabon mataimakin gwamna, Murtala Sule Garo.
A yayin jawabinsa, Ganduje ya gaishe da Sanusi tare da bayyana shi a matsayin shugaban Majalisar Sarakunan Kano.
Haka kuma wannan ne karo na farko da Ganduje ya amince da Sanusi a wannan matsayin tun bayan da ya tube shi daga sarautar Sarkin Kano a shekarar 2020 yayin da yake kan mulki.
Daga baya an mayar da Sanusi kan sarautarsa bayan dawowar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf kan mulki.
