Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, zai ci gaba da kasancewa a hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), bayan da babbar kotun jihar Kaduna ta ɗage yanke hukunci kan bukatar belinsa zuwa makon farko na watan Yuni.
Alƙalin kotun, Darius Khobo ne ya sanya ranar a yau Talata bayan sauraron hujjojin bangarorin a shari’ar, wadda ta shafi tuhume-tuhume guda tara da aka gyara, kan zargin zamba, cin amanar ofis da kuma rashawa.
ICPC ta riga ta gyara tuhumar, inda ta bar El-Rufai a matsayin wanda ake kara shi kadai a shari’ar.
A zaman da aka ci gaba da shi, an fi mayar da hankali ne kan bukatar beli da tsohon gwamnan ya gabatar, wadda bangaren masu gabatar da kara suka yi watsi da ita, suna cewa zai iya kawo cikas ga binciken da ake yi.
Sai dai kotun ta ɗage yanke hukunci kan bukatar, tare da umartar a ci gaba da tsare wanda ake kara a hannun ICPC har sai an yanke hukunci.
Lauyan wanda ake kara, Ukpong Akpan, ya soki matakin kotun, yana mai cewa ba shi da dalili kuma yana nuna akwai wasu matsaloli a ciki.
