Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya soki Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan cire tanadin tilasta tura sakamakon zaɓe ta nau’ra mai kwakwalwa a cikin gyaran Dokar Zaɓe da Majalisar Dattawa ta yi.
Da yake magana a wata hira da Trust TV, El-Rufai ya zargi Akpabio da hana aiwatar da gyaran tsarin zaɓe tare da yin aiki don kare muradun jam’iyyar mai mulki.
“Ai Majalisar Dattawa ba ita ce matsalar ba. Akpabio ne matsalar, shi bita zai zai ne a hannun Asiwaju. Ya kamata Majalisar Dattawa ta haɗa kai wajen adawa da wannan mataki lokacin da suka dawo aiki,” in ji El-Rufai.
Ya kuma kalubalanci matsayin Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa, yana mai nuni da tsohuwar alaƙar da ke tsakaninsu.
“Ban ɗauke shi a matsayin ‘distinguished’ ba mun san juna tun shekarun 1990s. Ina ganin na cancanci kiransa da sunansa na ainihi, kuma shi ya san dalilina,” ya ƙara da cewa.
Dangane da zanga-zangar ‘Occupy National Assembly’ da ke gudana, wadda mambobin jam’iyyarsa suka shiga, tsohon gwamnan ya ce da yana cikin ƙasar nan da ya halarci zanga-zangar tare da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi.
“Da ina cikin ƙasar nan, da na shiga zanga-zanga tare da Peter Obi a Majalisar Tarayya. Tura sakamakon zaɓe kai-tsaye ta lantarki zai hana maguɗi. Majalisar Wakilai ta amince da shi, amma abin takaici Majalisar Dattawa ta hana aiwatar da shi,” in ji El-Rufai.
