Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce idan har ana son yakin da ake yi da matsalar tsaro ya yi nasara dole sai an fara da manyan jami’an gwamnati.
Obasanjo ya ce magance rashawa daga sama zai zama izina ga wasu tare da tabbatar da adalci da kuma aiwatar da ayyukan gwamnati a bude.
Shugaban wanda ke magana a cikin wani shiri na wani gidan radio mai zaman kansa a Abeokuta, jihar Ogun, ya ce matsalar cin hanci da rashawa ta shiga kowane lungu kuma har sai an fara da manyan shugabanni za a samu nasara.