Hukumar ƴaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta tsare tsohon Ministan Ƙwadago kuma tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Chris Ngige, da safiyar ranar Alhamis.
Mai magana da yawun Ngige, Fred Chukwuelobe, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa:
“Ngige yana tare da EFCC. Ba a sace shi ba.”
Har yanzu EFCC bata bayyana dalilin tsare Ngige ba, amma ana sa ran hukumar za ta fitar da cikakken bayani nan gaba kan binciken da take yi a kansa.
Chris Ngige ya zama mutum na biyu daga cikin tsoffin ministocin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da hukumar EFCC ta tsare kwanan nan.
Kafin shi, tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, shima yana hannun EFCC.
