Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta rufe wani gida da ke da alaƙa da tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, SAN, a daren Laraba, a matsayin wani ɓangare na binciken cin hanci da rashawa da ake yi masa.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an EFCC tare da wasu jami’an tsaro sun isa gidan domin aiwatar da umarnin rufewa, inda a lokacin Nana Hadiza Buhari, ’yar tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Muhammadu Buhari kuma matar Abubakar Malami, take a cikin gidan.
Matakin da hukumar ta ɗauka na zuwa ne yayin da EFCC ke ci gaba da tsare Malami bisa zargin aikata laifukan cin hanci da rashawa, halasta kuɗaɗen haram, da kuma wasu laifuka da suka shafi kuɗaɗen marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Muhammad Sani Abacha, da aka kwato.
A cewar hukumar, belin da aka bai wa Abubakar Malami a baya an soke shi ne sakamakon rashin cika sharuddan belin da aka gindaya masa.
EFCC ta tabbatar da cewa har yanzu tsohon ministan yana tsare a hannun hukuma domin ci gaba da zurfafa bincike kan zarge-zargen da ake yi masa.
