Shugaban ƙaramar hukumar Gombi, Markus Ishaya, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce wasu mutane biyu sun jikkata kuma suna karɓar magani a asibitin Cottage da ke Gombi
Ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da wata mata, tare da ƙona cocin EYN, gidaje uku da kuma lalata shaguna biyu
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa maharan sun shiga kauyen da sanyin safiyar Litinin, inda suka fara harbe-harbe tare da kona gidaje
Harin ya zo ne kasa da makonni biyu bayan wani makamancinsa da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane goma a ƙaramar hukumar Hong ta jihar Adamawa
