
Majalisar ministocin ƙungiyar ƙasashen yammacin Afrika ECOWAS, ta gudanar da wani taro a Abuja, inda ta tattauna kan yadda za ta cike giɓin da ƙasashen Sahel 3 na Nijar, Mali da Burkina Faso suka haifar, lamarin da ke nufin maye gurbinsu a cikin zauren majalisar gudanarwar ƙungiyar.
A farkon wannan shekarar ne ƙasashen 3 da dukkaninsu sojoji ke mulka suka kammala ficewa daga ECOWAS a hukumance, bayan shafe shekara guda ana ƙoƙarin mayar dasu cikin haɗakar amma abu yaci tura.
Shugaban Majalisar ta ECOWAS Omar Alieu Touray yayin jawabi bayan tashi daga taron daya gudana a babban birnin Najeriya, ya ce tafiyar jami’an ƙungiyar da ke matsayin wakilcin ƙasashen 3 ya haddasa gagarumin giɓi wanda wajibi ne suyi gaggawar cike shi don tafiyar ayyuka yadda aka saba.
Tun bayan juyin mulkin ƙasashen 3 ne ake ganin takun-saƙarsu da ECOWAS wadda ta lafta musu takunkumai tare da matsin lamba don ganin ƙasashen sun koma turbar demokraɗiyya ciki har da barazana da ƙarfin soji