Shugaban Amurka Donald Trump ya ce alakarsa da tsohon mai ba shi shawara kuma shakikin abokinsa, babban attajirin duniya, Elon Musk ta kare – babu saura.
A lokacin wata tattaunawa da Trump din ya yi da kafar yada labarai ta NBC a ranar Asabar, ya ce babu wata magana ta sasanto a tsakaninsu daga yanzu.
Kalaman su ne na baya-bayan nan da shugaban ya yi kan irin sukar juna da tsofaffin abokan junan ke yi wa juna, tun bayan da aka samu sabani tsakaninsu game da shirin haraji na Trump din da kuma kudurin gwamnatin Amurkar na kasafin kudi.
Tun bayan da Elon Musk wanda a ‘yan kwanakin da suka gabata yake zaman tamkar dan-lele kuma kusa a gwamnatin Trump, da ke shugabantar sabuwar ma’aikatar da Trump ya samar tare da damka wa hamshakin attajirin hukumar ta Goge, ya ajiye mukamin aka fara sa-in-sa tsakaninsu.
Hukumar da ya damka masa wuka da dama don abin da shugaban ya kira inganta ayyukan gwamnati – wadda ta rika zaftare yawan ma’aikatan gwamnati da sunan tsuke bakin aljihu, ya raba gari da abokin nasa a alakar da ta taso tamkar ta auren zobe, suka rika caccakar juna a shafukansu na sada zumunta da muhawara.
Sabanin ya bayyana ne bayan da attajirin lamba daya a duniya – wanda ya bayar da madudin kudi a yakin zaben Trump, ya fito fili ya soki kudurin dokar da ke gaban majalisar dokokin kasar, na tsarin na Trump na haraji da da kashe kudade – kudurin da ke zaman wata babbar manufa ta cikin gida a gwamnatin.
Mafiya yawan ‘yan jam’iyyar Republican sun mara baya ga shugaban kasar, har ma mataimakin shugaban JD Vance, ya fito fili shi ma yana sukar Musk, inda ya bayyana shi da cewa ya harzuka ya kuma bar turba, yana abubuwan da suka saba wa hankali, kuma da wuya su sake karbarsa a tafiyarsu.
