Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2026 bayan amincewar da Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta ba shi.
Majalisar dokokin jihar ta amince da kasafin kuɗin a makon da ya gabata, inda jimillar kasafin ta kai naira biliyan 985.9.
A cewar bayanan kasafin, an ware naira biliyan 689.9, wanda ya kai kashi 70 na jimillar kasafin kuɗin, domin manyan ayyukan raya ƙasa, yayin da aka ware naira biliyan 287 domin gudanar da ayyukan yau da kullum.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da suka dauki hankalin jama’a a kasafin kuɗin shi ne ware naira miliyan 100 ga kowace gunduma daga cikin gundumomi 255 na jihar Kaduna, domin aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma daga tushe.
Da yake rattaba hannu kan kasafin kuɗin, Gwamna Uba Sani ya yabawa ’yan majalisar dokokin jihar bisa amincewa da kasafin cikin kankanin lokaci, inda ya bayyana hakan a matsayin alamar kyakkyawan haɗin kai da fahimta tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa.
Gwamnan ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da aiki kafada da kafada da Majalisar Dokoki da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da ci gaba mai dorewa da inganta rayuwar al’ummar jihar.
Wakiliyar mu, Hafsat Iliyasu Dambo, ta ruwaito cewa, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Dahiru Yusuf Liman, ya ce majalisar ta amince da kasafin kuɗin ne bayan cikakken bibiya da kare-karen kasafin da ma’aikatu da hukumomin gwamnati suka gabatar a gaban majalisar.
