Wani bincike da jaridar Dailytrust ta wallafa ya nuna cewa makarantun firamaren gwamnati da dama a Jihar Kano na fama da matsanancin ƙarancin malamai, inda a matsakaita malami guda ke kula da ɗalibai 105.
Rahoton ya ce kusan kashi 25 cikin 100 na makarantun firamare a jihar na da malami guda kacal da ke koyar da dukkan azuzuwan firamare shida. Haka kuma, binciken ya nuna cewa yawan ɗalibai a kan malami ya ninka adadin da ƙungiyar UNESCO ke ba da shawara a kai.
Masu ruwa da tsaki a fannin ilimi sun bayyana cewa wannan yanayi na shafar ingancin koyarwa da kuma sakamakon karatun yara, musamman a yankunan karkara inda ake fama da ƙarancin malamai fiye da birane.
Rahoton ya kuma nuna cewa baya ga ƙarancin malamai, makarantu da dama na fama da matsalolin rashin kayan koyo, cunkoson azuzuwa da kuma yawaitar rashin halartar makaranta daga wasu malamai da ɗalibai.
A nata ɓangaren, gwamnatin Kano ta ce tana ɗaukar matakan magance matsalolin ta hanyar ɗaukar sababbin malamai da kuma inganta ababen more rayuwa a makarantun gwamnati.
