Dubban mutane sun fito kan tituna a faɗin Isra’ila, don adawa da matakin gwamnatin ƙasar na faɗaɗa farmakin sojin da take a Gaza.
A ranar Juma’a ne majalisar tsaron Isra’ila ta amince da sharuɗa biyar na kawo karshen yaƙin, ciki har da shirin karɓe iko da Birnin Gaza, inda sojojin Isra’ilar suka ce za su “shirya karɓe iko” da Gaza baki ɗayanta.
Masu zanga-zangar da suka haɗa da iyalan mutum 50 ɗin da ake garkuwa da su a Gaza – ciki har da 20 ɗin da ake kyautata zaton suna raye, suna fargabar cewa shirin zai saka rayuwar ƴan uwansu cikin haɗari, inda suka buƙaci gwamnatin Isra’ila da ta yi ƙoƙarin don ganin an sake su.
Shugabannin Isra’ila sun yi watsi da sukar da ake yi wa shirinsu, inda Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce “hakan zai taimaka a saki mutanen mu”.
Wata ƙungiya da ke wakiltar iyalan waɗanda ake garkuwa da su ta wallafa a shafin X cewa: “Faɗaɗa farmakin zai saka mutanen mu da kuma sojoji cikin barazana – al’ummar Isra’ila ba su da niyyar saka su cikin haɗari”.
