
Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun sake cafke wani da ake zargi da garkuwa da mutane a cikin alhazai na kan hanyarsa na zuwa hajji.
Mutumin da aka kama shine Sani Galadi, an kuma shi ne a filin jirgin saman Sultan Abubakar da ke Sokoto, a ranar Litinin da misalin karfe 11:15 na safe.
Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, Galadi ya shiga hannun jami’an DSS ne yayin da ake gudanar da tantance maniyyatan hajji a filin jirgin.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun dade suna bibiyar motsinsa kafin a kama shi a lokacin da yake yunkurin barin ƙasar domin gudanar da aikin hajji.
“Galadi na daga cikin jerin sunayen da hukumomin tsaro suka ayyana a matsayin “wanda ake nema ruwa a jallo” bisa zargin hannu a garkuwa da mutane a jihohin Abuja da Kogi.
Kama Galadi na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan kama wani shahararren mai garkuwa da mutane a sansanin alhazai da ke Abuja, wanda shi ma ake zargin yana kokarin tserewa zuwa Saudiyya.
Wata majiya mai karfi daga cikin jami’an tsaro ta tabbatar da kama wanda ake zargin, inda ta ce, “an samu nasarar cafke shi ne a wani aiki na sirri da aka kaddamar domin tsarkake ƙasar nan daga miyagun laifuka.”
Hukumar DSS na daga cikin manyan hukumomin leken asiri a ƙasar, kuma a ‘yan watannin nan ta ƙara kaimi wajen kama wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka, musamman masu garkuwa da mutane da ke addabar al’umma a sassa daban-daban na ƙasa