
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya dakatar da rangadin da yake yi na kasar hakiman dake karkashin masarautar Kano sakamakon rasuwar Aminu Dantatta.
Sarkin ya sanar da hakan ne a garin Dawakin Tofa a ranar Asabar a jawabinnsa ga al’ummar da taru yana mai nuna alhinin na rashin dattijon attajirin da kuma allakarsa da gidana sarautara Kano.
Sarkin ya isa garin Dawakin Tofa a ranar Juma’a ya wayi gari ranar Asabar domin yin rangadin Tofa a wannan rana sannan ya wuce Rimin Gado da kuma Kabo a ranar Lahadi.

Amma sakamako rasuwar sarkin ya katse ranagadin a garin Tofa wanda daga nan zai juyo Kano har sai an share makoki.
Sarkin ya ba al’ummar Rimin gado da kuma Kabo hakuri na dage rangadin kasashen hakiman nasu zuwa wani lokaci nana gaba.
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi ya soma rangadin ne a Danbatta a inda ya kuma ziyarci Kananan Hukumomin Makoda da Minjibir da Ungoggo, da kuma gundomin Kunya da Zaura BabAba.
A dukkannin wadanan wurare dubban al’umma ne suka taru don tarbar sarki cike da murnar da farin ciki