Mataimakin Gwamnan Kano Alhaji Murtala Sule Garo ya karbi bakuncin takwaransa na jihar Sokoto, Injiniya Idris Muhammad Gobir, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ci gaba da shugabanci na gari ga al’ummar su.
Yayin ganawar, wadda ta gudana a gidan gwamnatin Kano, bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi kyautata alaka da hadin gwiwa tsakanin jihohin Kano da Sokoto, tare da yi musayar ra’ayoyi kan hanyoyin bunkasa ci gaba da walwalar al’umma.
Ziyarar dai na daga cikin kokarin karfafa dangantaka tsakanin gwamnatocin jihohin biyu da inganta hadin kai wajen aiwatar da manufofin ci gaba.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito, Mataimakin Gwamnan na Sokoto Injiniya Idris Muhammad Gobir na bada tabbacin cewa jihar Sokoto zata ci gaba da yin haɗin gwiwa da Kano ta kowace fuska domin tabbatuwar samun nasarar gwamnatocin biyu.
