
Kamfanin Dangote da ya mallaki matatar mai ta Dangote ya sanar da sabon ragin farashin man fetur a gidajen da ke hulɗa da su.
Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis ya ce, ragin ya bambanta daga yankunan ƙasar daban-daban.
Kamfanin ya ce, za a riƙa sayar da litar mansa a Legos kan naira 875, yayin da za a riƙa sayar da litar a jihohin arewa maso yamma kan naira 895, sai kuma naira 905 a jihohin arewa maso gabashin Najeriya.

A cewar matatar, abokan huldar sun haɗa da gidajen man kamfanonin: MRS, AP, Heyden, Optima, TechnOil, da Hyde.
Matatar ta yi kira ga sauran ‘yan kasuwa da su haɗa kai da abokan hulɗarta, ta yadda za su nuna goyon bayansu ga manufofin farko na Shugaba Bola Tinubu, da ke ba da shawarar ba da fifiko ga kayayyaki da ayyuka da ake samarwa a cikin gida.
Tun lokacin da ta fara aiki, matatar man Dangote ta ci gaba da aiwatar da dabarun rage tsadar kayayyaki da nufin sauƙaƙawa ’yan Najeriya.
A watan Fabrairun 2025, kamfanin ya yi ragin farashin man fetur sau biyu, wanda ya haifar da raguwar jimillar Naira 125 kan kowace lita.
Hakan ya biyo bayan ragin kusan Naira 45 a kowace lita a watan Afrilu.