Matatar Dangote ta yi gargaɗin cewa farashin litar fetur a Najeriya na iya haura N1,400 idan ƙasar ta koma dogaro kacokan da shigo da mai daga waje.
Matatar ta bayyana cewa samar da mai a cikin gida shi ne muhimmin ginshiƙi wajen daidaita farashi da hana tashin gwauron zabi a kasuwa.
Matatar Dangote ta bayyana hakan ranar Litinin, inda ta karyata rahotannin cewa za a dakatar da aiki don gyara, tana mai cewa rahotannin ƙarya ne da aka yaɗa don ba da hujjar ƙara farashin fetur.
A cikin wata sanarwa, matatar ta ce idan ba don ayyukanta na cikin gida ba, masu shigo da mai daga waje za su ci gaba da yin abin da suka ga dama, abin da zai iya daga farashin fetur har zuwa N1,400 kan kowace lita.
Sanarwar ta ƙara da cewa ayyukan matatar sun taimaka wajen daidaita kasuwar man fetur, tare da rage tasirin masu shigo da mai daga waje da ke neman riba ba tare da la’akari da halin da jama’a ke ciki ba.
