Ahmad Hamisu Gwale
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, ta cimma yarjejeniya da FK Radnički Niš ta kasar Serbia, domin dan wasa Abba Adam Oscar ya koma kungiyar a matsayin aro.
Sashen yada Labarai na Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ne ya sanar da komawar dan wasan a wata sanarwa a ranar Asabar.
Abba Oscar, ya koma kungiyar ta kasar Serbia a matsayin aro, da zaɓin siyar da dan wasan idan bukatar hakan ta taso.
Haka zalika Abba Oscar, ba zai buga wasan da Kano Pillars za ta karbi bakunci Abia Warriors a wasa mako na 24 da zasu kece raini a yau Asabar a filin wasa na Sani Abacha.
Ɗan wasan wanda kawo yanzu haka, ya zura kwallaye biyar a gasar NPFL ta bana, zai koma kasar Serbia a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar bana.
Kwallaye biyu da dan wasan ya zura kuma ake tunawa dashi, sune yadda ya zura kwallo biyu a wasan da Kano Pillars ta do ke Enyimba da ci 2-1 a gasar Firimiyar Najeriya ta bana a filin wasa na Sani Abacha.
