
Wani dattijo mai shekara 72 da ’ya’yansa biyu sun gurfana a gaban Kotun Majistire mai lamba 28 da ke garin Gano bisa zargin sayar da miyagun ƙwayoyi.
Iyalin mazauna Unguwar Makera a Karamar Hukumar Dawakin Kudu suka gurfanar da su bayan korafin da al’ummar yankin karkashin jagorancin hakimin Tamburawar Dan-Tube Alhaji Auwalu Umar
Rahotanni sun nuna cewa rikici ya barke ne lokacin da shugaban kungiyar sa-kai na yankin ya yi wa dattijon gargadi da ya daina sayar da miyagun ƙwayoyi. Hakan ya janyo rikici tsakaninsa da ’ya’yan dattijon, sakamakon da guda daga cikin ’yan sa-kai ya ji rauni.
A yayin zaman kotun a gaban Majistire Malika Muhammad da iyalan wadanda ake tuhuma sun nemi sulhu da wadanda suka kai ƙara.
Kotun ta bayar da belinsu bisa wasu sharudda masu tsauri, ciki har da cewa dattijon mai shekara 72 dole ne ya halarci kowanne zama da kansa.