Majalisar wakilai ta shaida wani sabon sauyin siyasa a yau Talata, inda yan majalisa 17 suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar Congress ADC zuwa NDC a zaman majalisar.
Yan majalisar sun ce sun dauki wannan mataki ne sakamakon rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam’iyyarsu ta baya daga matakin kasa har zuwa matakin gunduma.
Daga cikin wadanda suka sauya sheka akwai Yusuf Umar Datti, mai wakiltar mazabar Kura/Madobi/Garun Mallam daga jihar Kano, wanda ya ce rashin daidaito a cikin ADC ya hana shi gudanar da aikinsa yadda ya kamata ga al’ummarsa.
Haka kuma, Harris Okonkwo, mai wakiltar Idemili ta Arewa da ta Kudu a jihar Anambra, ya ce an dauki matakin ne bayan tuntuba mai zurfi da masu ruwa da tsaki da kuma al’ummar mazabarsa.
Sauran yan majalisar da suka koma NDC sun hada da Sani Adamu (Minjibir/Ungogo, Kano), Thaddeus Attah (Eti-Osa, Legas), Mataimakin bulalar yan adawa George Ozodinobi (Njikoka/Anaocha/Dunukofia, Anambra), Lilian Obiageli (Awka ta Arewa da ta Kudu, Anambra), da OluwaSeyi Sowunmi (Ojo, Legas).
Sauran sun hada da Peter Anekwe (Anambra ta Gabas/Yamma), Zakari Umar Mukhtari (Tarauni, Kano), George Olawande (Amuwo Odofin, Legas), Murphy Osaro Omoruyi (Egor/Ikpoba-Okha, Edo), Umezuruike Manuchim (Port Harcourt I, Ribas), Emeka Idu (Onitsha ta Arewa/Kudu, Anambra), da Jesse Onuakalusi (Oshodi-Isolo, Legas).
Haka kuma akwai Ifeanyi Uzokwe (Nnewi ta Arewa/Kudu/Ekwusigo, Anambra), Afam Ogene (Ogbaru, Anambra), da Kamilu Ado (Wudil/Garko, Kano).
A wani bangare na daban, Leke Abejide, mai wakiltar mazabar Yagba, shi ma ya sanar da ficewarsa daga ADC zuwa jam’iyyar APC.
Wasu yan majalisa sun nuna damuwa kan yadda sauyin jam’iyya ke karuwa gabanin zaben shekarar 2027, inda suka ce rikici a cikin jam’iyyu na daga cikin manyan dalilan da ke haddasa hakan.
Kakakin majalisar ya karbi wasikun sauyin shekar tare da yi wa yan majalisar fatan alheri a sabbin jam’iyyunsu, kamar yadda al’adar majalisa ta tanada.
Ana sa ran wannan mataki zai sauya tasirin jam’iyyun adawa a majalisar, musamman ma rage karfin jam’iyyar ADC a majalisar wakilai.
