
Dakatar da shirye-shiryen siyayasa kai tsaye a gidajen radio a jihar Kano na kara samun goyon baya.
Goyon baya ga wannan mataki na baya-bayan nana ya fito ne daga Majalisar Shawara a tsakanin Jam’iyyu ta jihar Kano (IPAC).
Shugaban IPAC na jihar Kano, Alhaji Isah Nuhu Isah, ne ya bayyana hakan a yayin wani wani taron manema labarai da suka gudanar a birnin Kano inda ya bayyana matakin a matsayin mai matukar muhimmanci wajen kare zaman lafiya da inganta aikin jarida na gaskiya.
“Matakin dakatar da shirye-shiryen siyasa na kai tsaye ya yi daidai da manufofin IPAC, na inganta muhawarar jama’a bisa ka’ida da kuma tabbatar da zaman lafiya a harkokin siyasa tsakanin dukkan jam’iyyu a jihar”. In ji shi.
IPAC ta bukaci ‘yan siyasa da al’umma su fahimci wannan dakatarwa a matsayin lokaci na nazari ba a matsayin kakkabe ‘yancin faɗar albarkacin baki ba, duba da lokacin zaɓen 2027 ya tunkaro, a don haka suka roƙi duk masu ruwa da tsaki a siyasa da su yi yakin neman zabe bisa batutuwa masu amfani kuma su guji kalaman tunzuri domin sauya yanayin siyasar jihar.