
Dakarun haɗin gwiwa na Operation Hadin Kai a arewa maso gabashin Nijeriya sun ce sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram 17 a wasu hare-haren da suka kai a jihohin Borno da Adamawa.
Muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na soji, kaftin Reuben Kovangiya, ya bayyana a wata sanarwa cewa ‘yan ta’addan suna aika-aika ne a ƙananan hukumomin Bama da Konduga da Gwoza da Magumeri da kuma Biu na jihar Borno da kuma ƙaramar hukumar Michika a jihar Adamawa.
Ya ce dakarunsu sun gano tare da fasa bama-bamai fiye da 14 da ‘yan ta’addan suka ɗana a wurare daban daban.
Kovangiya ya ƙara da cewa a lokacin samanen, dakarun sun taimaka wajen mayar da ‘yan gudun hijira 987 gidajensu a Mandaragirau da ke ƙaramar hukumar Biu.
A cewarsa dakarun sun aiwatar da ayyukan tare da dakarun ƙasar Nijar a yankunan Diffa da Duji-Damasak, inda suka inganta tsaro da kuma kwanciyar hankali a wuraren.