
Hukumar NECO ta sanar cewa daga watan Nuwamba zuwa Disamba 2025, za a fara amfani da Computer-Based Test (CBT) wajen rubuta jarabawar kammala sakandire ta kasa.
Hukumar ta bukaci masu cibiyoyin CBT masu zaman kansu da su yi rijista da sharuddan tsaro da kayan aiki da aka tanada, don shiga tsarin.
A tattaunawa da wakilyarmu Halima Ayyuba, Farfesa Ahmad Iliyasu na Jami’ar Bayero ya gargadi cewa tsarin CBT babban kalubale ne ga dalibai da dama, musamman wadanda basu saba amfani da kwamfuta ba.
“Dole ne a shirya tsarin sosai kafin fara amfani da shi, domin gujewa matsalolin faduwar jarrabawa kamar yadda ake gani a JAMB,” in ji shi.