Gwamnatin Jihar Kogi ta amince da ƙara shekarun ritayar ƙwararrun ma’aikatan lafiya daga 60 zuwa 65, ko kuma daga shekaru 35 zuwa 40 na aiki, gwargwadon wanda ya fara cika.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya ce Gwamna Ahmed Usman Ododo ya amince da matakin ne domin riƙe ƙwararrun ma’aikatan lafiya da inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.
Ya bayyana cewa sabon tsarin ya shafi ƙwararrun ma’aikatan lafiya da ke aiki a manyan asibitoci, asibitocin gwamnati da cibiyoyin kula da lafiyar jama’a.
Shugabar ma’aikatan gwamnatin jihar, Falilat Yusuf Musa, ta yaba da matakin, tana mai cewa zai taimaka wajen ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata da kuma bai wa matasa damar koyon aiki daga manyan ma’aikatan da suka daɗe suna hidima.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abdulazeez Adams Adeiza, ya ce matakin zai ƙara ƙwarin gwiwar ma’aikatan lafiya tare da inganta ci gaba da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga al’ummar jihar.
