Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da samun sabbin rahoton kamuwa da cutar shan inna (polio) a jihar.
An gano sabbin kamuwar cutar ne yayin wani sabon zagaye na rigakafin cutar shan inna da gwamnati ta shirya domin yi wa yara miliyan 1.4 allurar rigakafi a fadin jihar.
Manajan ayyukan cibiyar kula da harkokin gaggawa ta Emergency Operations Centre (EOC) a Zamfara, Dr. Murtala Salaudeen, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin cibiyar.
Ya ce domin tabbatar da cewa babu wani yaro da ya rage ba tare da an yi masa rigakafi ba, an tura ma’aikata 1,997 zuwa sassa daban-daban na al’ummomin jihar domin gudanar da aikin.
Dr. Salaudeen ya ce a wannan karon sun tsara aikin ta hanyar ziyarar gida – gida, inda ake kuma ba kowane yaro da aka yi wa rigakafi kunshin indomie domin karfafa gwiwar iyaye su fito da yaransu.
Ya bayyana cewa wannan zagaye na rigakafin ya fara ne daga 7 zuwa 13 ga Maris, 2026, kuma yana da nufin tabbatar da cewa dukkan yara sun samu kariya daga cutar.
A cewarsa, yara hudu da cutar shan inna ta kama da aka samu sun fito ne daga kananan hukumomi biyu na jihar, inda uku daga cikinsu suka fito daga Karamar Hukumar Gummi, yayin da daya kuma ya fito daga Karamar Hukumar Tsafe.
Ya kara da cewa a shekarar 2024 an samu kamu 16 na cutar shan inna a jihar, yayin da a shekarar 2025 ba a samu ko guda ba.
Dr. Salaudeen ya jaddada muhimmancin yi wa yara rigakafin cutar, yana mai cewa magungunan rigakafin lafiyayyu ne kuma ba sa cutar da yara, sai dai suna taimakawa wajen kare su daga cutar shan inna.
Ya kuma ce dukkan masu ruwa da tsaki suna da muhimmiyar rawa wajen yakar cutar, kuma gwamnati za ta ci gaba da aiki tare da abokan hulda domin tabbatar da nasarar shirin.
