
Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) ta tabbatar da bullar cutar Kyandar Biri (Mpox) a karamar hukumar Ungogo a inda mutane biyu suka kamu.
Daraktan cibiyar, Farfesa Muhammad Adamu Abbas ne ya bayyana hakan yayin taron karawa juna sani na kwana guda da aka gudanar a jihar.
Shugaban ya bukaci al’umma da su kasance masu sa ido tare da sanar da hukumomi duk lokacin da aka fuskanci wata cuta da ba a kai ga ganowa ko fahimtar ta ba.
“Hakan zai taimaka wajen daukar matakan gaggawa don dakile yaduwar cututtuka domin a yanzu haka hukumar na da ma’aikata fiye da 100 da ke aikin sa ido da tattara bayanai daga sassa daban-daban na Kano domin gano yiwuwar bullar kowace irin cuta.” In ji shi.
Farfesa ya kuma ce, cibiyar ta fara hadin gwiwa da tashoshin motoci jihar domin samun sahihan bayanai da kuma saurin gano matafiya masu alamun cututtuka, musamman masu bukatar kulawar gaggawa.
Ya kuma kara da cewa matakin da suke dauaka yana daga cikin kokarin tabbatar da lafiyar jama’a da kuma dakile yaduwar cututtuka kafin su zama barazana ga al’umma.
Wannan na zuwa ne kasa da wata guda da samun rahoton farkon bullar cutar, sai dai hukumar ta ce an shawo kan lamarin kafin ta yadu zuwa sauran sassa jihar.