
Aƙalla mutane 346 ne suka rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar cutar kwalera a Khartoum babban birnin Sudan, yayin da ɗaruruwan wasu suka kamu da cutar.
Rahotanni sun bayyana cewa cutar na ci gaba da yaɗuwa, inda ake samun sama da sabbin mutane 80 da ke kamuwa da cutar a kullum.
Shugaban Ma’aikatar Lafiya ta Khartoum Fath Al-Rahman Al-Amin, ya sanar da kafa cibiyoyin killace marasa lafiya guda 15 domin daƙile yaɗuwar cutar.
A ranar 14 ga Mayu, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa ta mika kaya masu nauyin tan 15 na kayan lafiya ga Ma’aikatar Lafiya ta Khartoum, domin tallafa wa ƙoƙarin dakile annobar.
Ma’aikatar Lafiya ta Sudan ta sanar da shirin ƙaddamar da kamfen ɗin rigakafin kwalera a yankin, domin rage yaɗuwar cutar da kare lafiyar jama’a.
Hukumomin kiwon lafiya na ci gaba da kokarin shawo kan lamarin, yayin da ake fargaba kan yawaitar kamuwa da cutar a cikin al’umma.