Daga Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya umurci Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Jihar Kano (KNCDC) da ta gudanar da kidayar cutar karzuwa da ke addabar Almajirai a fadin jihar.
Shugaban hukumar, Farfesa Muhammad Adamu Abbas ne ya bayyana haka yayin taron wayar da kan Almajirai a makarantar Tahfizul Qur’an Madarasatul Umar Farouk, dake Hausawar Dan Fulani a Karamar Hukumar Tarauni.
”Gwamnan ya bayar da umarnin ne ta hannun Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, na mu tattara bayanan wadanda suka kamu da cutar zazzaɓi da sauran cututtukan fata daga watan Janairu zuwa yanzu”.
”An gabatar da rahoton da ya shafi watan Janairu zuwa Oktoba, yayin da ake kammala tattara bayanan na Nuwamba don gabatar da su.
”Manufar gwamnan ita ce tabbatar da cewa an samar da magunguna ga marasa lafiya dake makarantun Almajirai da zarar an kammala tattara bayanan”. In ji shi.
Tun da farko, shugaban hukumar ta KNCDC, ya bayyana cewa gudanar da aikin wayar da kan jama’a a karamar hukumar ya zama dole saboda shigowar sanyi, wanda a lokuta da dama yakan haifar da cututtukan fata.
A nasa bangaren, shugaban makarantar, Malam Ahmad Abubakar ya gode wa KNCDC da kuma gidauniyar Zayti da suka fadakar da daliban kan rigakafin cututtuka.
Malamin ya kuma yaba da kayayyakin da aka bayar tare da ba da tabbacin cewa makarantar za ta ci gaba da tallafawa kokarin da ake na kare lafiyar dalibanta.
Malam Ahmad Abubakar ya kara da cewa makarantar tana da dadadden tarihi, wanda ta shafe sama da shekaru 50 a duniya.
Taron wayar da kan almajiran na hukumar ya gudana ne tare da hadin gwiwar Gidauniyar Zayt. Sun kuma rarraba barguna da rigunan sanyi da garin kunu ga almajiran.
