Tsohon Mataimain Shugaban kasa kum tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, yanzu kuma a jigo a jamiyyar ADC, Atiku Abubakar ya bayyana zargin cushe a dokar haraji da Tinubu ya saw a hannu da cewa cin amanar ƴan ƙasa ne.
Atiku ya bayyana haka ne a shafinsa na dandalin sada zumunta a ranar Talata.
“Sauye-sauyen da aka samu sun nuna cewa gwamnatin ta fi mayar da hankali ne kan tatsar ƴan ƙasar sama da taimakonsu.” In ji shi.
Jigon siyasar hamayyar ya yi kira da a dakatar da aiwatar da aiwatar da dokar harajin, wanda ake sa ran farawa a watan Janairun domin gudanar da cikkaken bincike.
Ya kuma bukaci majalisar dokokin ƙasar ta yi gaggawar gyara sauye sauye da aka yi ba bisa kaida ba, sannan a hukunta masu hannu a yi wa kundin tsarin mulki zagon ƙasa, sannan hukumar EFCC ta gudanar da bincike kan su.
