 
        Babban Bankin Kasa (CBN) ya saki Dala Biliyan 1.259 ga ‘yan kasuwa masu shigo da man fetur da dangoginsa a tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2025, a cewar sabbin bayanan gwamnati’
Matakin na zuwa ne duk da cece-kuce kan ci gaba da dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen ƙetare, duk da fara sarrafa mai a matakin kasuwanci daga Matatar Dangote.
Sabbin bayanai daga Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur sun bayyana cewa sama da kashi 69 na lita biliyan 21 da aka ci gaba da amfani da su a faɗin ƙasa daga watan Agusta 2024 zuwa farkon watan Oktoba 2025 an shigo da su ne daga ƙasashen waje.
Duk da iƙirarin matatar Dangote cewa tana da isasshen ƙarfin samarwa don biyan buƙatun cikin gida har ma da na fitarwa.
A cikin watanni uku na farko na 2025 kaɗai, ‘yan kasuwa sun shigo da lita biliyan 2.28 na man fetur, wanda ya zama mafi ƙaranci daga cikin adadin shigo da mai a kowace shekara a baya-bayan nan.
Masana sun bayyana cewa wannan na nuna raguwar dogaro da waje, amma har yanzu shigo da mai na ci gaba da daɗa tasiri.
Mai magana da yawun ƙungiyar (IPMAN), Chinedu Ukadike ya ce, farashi ne kaɗai ke ƙayyade inda za a samo man fetur.
Masana na ganin cewa har sai matatun cikin gida sun kai matakin cikakken aiki, ’yan kasuwa za su iya tsayar da ra’ayi kan sayen man cikin gida da na waje, gwargwadon inda farashi ya fi araha.

 
           
           
           
           
         
         
         
         
         
         
           
          