
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙaddamar da gangamin wayar da kan al’umma kan illar wulaƙanta takardar kuɗi ta Naira, tare da gargadin cewa duk wanda aka samu da aikata irin wannan laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani ƙarƙashin dokar ƙasa.
An kaddamar da gangamin ne a kasuwar baje-koli ta ƙasa da ƙasa a Abuja, inda jami’an CBN suka shaidawa ‘yan kasuwa da jama’a cewa matakin ya zama wajibi ne domin kare darajar kuɗin ƙasa da kuma dakile asarar kuɗaɗe da gwamnati ke fuskanta wajen sabunta su.
“Wulaƙanta kuɗin Naira kamar liƙa su a bukukuwa da yaga kudin ko rubutu a kansu da kuma yadda ake cuɗanya da su ba tare da mutuntawa ba, na haifar da gagarumar matsala ga tattalin arziki, kuma yana rage tsawon lokacin amfani da kuɗin.”
CBN ya yi gargadin cewa masu karya doka za su iya fuskantar ɗaurin watanni shida a gidan yari ko kuma tarar da ta kai Naira dubu 50 a karkashin dokokin da ake da su.