Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka (AU), Moussa Faki Mahamat, ya karyata ikirarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa akwai kisan kiyashi kan Kiristoci a arewacin Najeriya.
Trump ya yi wannan ikirari yana mai cewa “‘Yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi na kaiwa Kiristoci kisan kiyashi” a Najeriya, tare da barazanar yi wa ƙasar farmaki.
Amma a yayin jawabi ga manema labarai a New York ranar Laraba, Faki ya ce ya kamata a yi taka-tsantsan wajen yin irin wannan maganganu.
Ya bayyana cewa mafi yawan wadanda aka kashe a rikicin arewacin Najeriya shi ne Musulmai, ba Kiristoci ba, kuma akwai kwararan hujjoji da ke nuna hakan.
Tun daga shekarar 2009, rikicin Boko Haram ya kashe sama da mutane 40,000 a Najeriya, tare da tilasta wa fiye da miliyan biyu barin gidajensu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya (UN).
